Commons:ISA Tool/ha
Ƙara bayannai da aka tsara zuwa fayiloli a kan Commons a hanya mai sauƙi da nishaɗi!

ISA kayan aiki ne na nishadi, Mai harsuna da yawa,ta wayar hannun-farko microcontributions kayan aiki ne, wanda ke sauƙaƙa wa(ƙungiyoyin marasa ƙwarewan) mutane don ƙara Structured data zuwa hotuna akan Wikimedia Commons
Tare da ISA, zaku iya zaɓar hotunan da aka riga aka ƙayyade su a kan Commons sannan ku nemi masu ba gudummawa su 'tag' din wannan tare da tsarin metadata na harsuna da yawa. Ana ƙirga maki ga kowane gudummawa, saboda haka yana yiwuwa a shirya 'tagging' ko gasa ta microcontributions ko ƙalubale tare da ISA.
An gina ISA tun asali ne don samar da ingantattun bayanai na harsuna da yawa da tsararrun bayani na Wiki Loves Africa hotuna. Amma kuma an haɓaka shi don ya zama mai amfani ga duk Wiki Loves X competition, kuma daga ƙarshe ya zama ana nufin all media files akan Wikimedia Commons.
An samar da ISA ne a matsayin haɗin kai tsakanin Wiki in Africa, Histropedia da Tsararren Bayanai akan aikin commons. GLAM Wanda akayi don Tsare-tsaren Bayanai akan Wikimedia Commons. Cigaba da gudanarwa da sadarwa na kayan aikin ISA yana hannu tawagar Wiki In Africa.
Yadda yake aiki?
An tsara kayan aikin don zama masaukin kananan gasa!
Wikimedians (masu shiryawa) na iya ƙirƙirar kamfen don inganta ɗaya ko wasu takamaiman nau'ikan hotuna akan Wikimedia Commons, a cikin wani ƙayyadadden lokaci . Ana ba da bayani a kan kayan aikin don saukin juya wannan kamfen ɗin zuwa ƙaramin gasa.
Sa'an nan (mahalarta) wikimedians na amfani da kayan aiki don inganta kwatancen hotuna da aka haɗa a cikin wannan camfen.
Kayan aiki yana ba da iKon ƙididdiga waɗanda ke ba da damar gano mafi kyawun masu ba da gudummawa ga yakin da aka faɗi a ainihin lokacin. Ana ba da bayanan mahalarta a cikin tsari mai kyau wanda za'a iya amfani dashi kai tsaye don haɗa rahotonin mai shiryawa ko amfani dashi don isar da sakamakon gasar a kan kafofin sada zumunta, juya kamfen ɗin zuwa kayan aikin sadarwa!
Bayanai mahalarta na samuwa don saukewa cikin tsarin cvs don kowane ƙarin amfani na ƙididdiga.
Ziyarci ISA Manuals don Yan wasa da Masu Gudanarwa don ƙarin cikakkun bayanai.
Inganta kayan aiki
An sanar da sigar farko ta kayan aikin a wajen Wikimania ta shekarar 2019.
An ƙara haɓaka kayan aikin yayin aikin R&D a cikin shekarar 2022-23. Duba 2022-2023 Aikin R&D: Tagging na kwamfutaSpecial:MyLanguage/Commons:ISA Tool/Image to Concept
An shirya hackathon a cikin watan Janairu shekarar 2024 don inganta kayan aiki: Wiki Mentor Africa Hackathon 2024.
Za'a iya samun source code a Nan:
- Phabricator ISA : https://phabricator.wikimedia.org/tag/isa/
- Bincika lambar : https://github.com/wikimedia/labs-tools-Isa
- Ka Bada gudummawa ga lambar: https://gerrit.wikimedia.org/r/#/admin/projects/labs/tools/Isa
- Taimaka wajen fassarar kayan aikin: https://translatewiki.net/wiki/Translating:ISA
ISA a labarai
Labari na Diff (13 Maris 2024)
Wiki Mentor Africa Hackathon 2024 (19-21 Janairu 2024)
GlamWiki thread on Twitter game da Tsarin Bayanai akan ayyuka Kai tsaye na Commons (Maris 2020)
Gabatar da ISA - kayan aiki mai kyau don ƙara tsarraren bayanai akan Commons (Nuwamba 2019)
GLAM Newsletter (Afrilu 2019)
Tutorial Videos
* A Tutorial video about how to use ISA Tool as a participants. (This video explains what structured data is, what ISA is, and how to add structured data using ISA.)
* A tutorial video about how to create ISA campaign as a campaign manager.
Shafuka masu alaƙa
Kayan aiki: https://isa.toolforge.org/
FASSARA: babban Shafi akan TranslateWiki
Shafin ayyukan Phabricator
TOOLHUB: ISA on ToolHub
STATS: Commons:ISA Tool/Stats
Wasu daga cikin nasarorin ISA.

- ISA ta karɓi kayan aikin mafi kyau Kyautar WikidataCon 2019!

- ISA ta karbi Mafi kyau kwarewa a Wikimania 2024, matsayi Eggbeater !
Menene Ake nufi da "ISA"
'Isa' kalmar yaren ChiShona ne don 'sanya' ko 'wuri', amma kuma tana iya aiki a matsayin acronym don Saurin Tsarin Bayanai, Ƙarin Tsarin Bayanai da sauransu.
Kyautar Mai haɓaka
- Shiga cikin ci gaban farko na habakawa

- Florence Devouard, development process lead, Wiki In Africa
- Islahaddow, communications lead, Wiki In Africa
- Eugene Egbe, Developer
- Navino Evans, Technical manager, Histropedia
- Sean McBirnie, Designer, Histropedia
- Mark Holmquist, Development advisor
- Sandra Fauconnier, mentor and SDC liaison, Wikimedia Foundation
- Shiga cikin Karin ci gaba (2022-23)
- Beat Estermann - Project Coordinator
- Eugene Egbe (contractor WMSE) - Software Development
- Matthias Ruediger (BFH) - Software Development
- Navino Evans (contractor WMSE) - Software Project Manager / Software Architect
- Sebastian Sigloch (SWITCH) - Representative Funding Institution
- Sebastian Berlin (WMSE) - Software Development
- André Costa (WMSE) - Coordination on the side of WMSE
- Florence Devouard (contractor WMSE) - Community Outreach
- Shiga cikin habakawa na farko (2023-24)
Masu amfani da kayan aiki na ISA

Almara ne abubuwa masu amfani da suke tafe don taimakawa wajen tunanin yadda kayan aikin ISA zasu iya taimaka maka a matsayin mai tsara kamfen ko dan wasa, kuma a gaskiya, akwai wasu ra'ayoyi masu yawa fiye da waɗannan.
Misali
: Wiki Loves Africa 2014 a Najeriya Edit-a-thon .
Kungiyar Najeriya sun shirya wani kamfen ta amfani da ISA don haɓaka kwatancen hotuna daga Wiki Loves Africa 2014. Wani mai gudanarwa ya kafa kamfen din edit-a-thon na kwana ɗaya a ranar Asabar. Rukuni daya kacal ne za a jera a cikin kayan aiki: Category:Hotuna daga Wiki Loves Africa 2014 in Nigeria.Mahalarta sunyi gasa don inganta bayanin hoto a cikin sa'a da aka sadaukar. Mai gudanarwa yana lura da ƙididdiga na mahalarta a ainihin-lokaci. An bayyana manyan masu cin nasara guda 5, kuma an bayar da kyaututtuka. Shafin Facebook ya bayyana sakamako, kuma mahalarta zasu iya sauke bayanan shiga don ƙarin bincike.
Misali
: Editocin masu magana da Faransanci turi
Editocin da ke magana da Faransanci sun fara kamfen don inganta tsarin bayanin Wiki Loves Africa 2015 hotuna daga ƙasashen da ke magana da Faransanci.
Misali
: Kampen Wayar da Kan Muhalli
Kungiyar muhalli ta duniya tana shirin gudanar da kamfen ta amfani da ISA don inganta metadata don hotuna masu alaƙa da lamuran muhalli. Kamfen ɗin yana da niyyar shigar da mahalarta a duk duniya wajen sanya alama da inganta bayanin hotuna na nau'in da ke cikin haɗari, gurɓataccen yanayi, da ƙoƙarin kiyayewa. Masu tsarawa sun ƙirƙiri kamfen ɗin, sun saita takamaiman rukuni, kuma suna ƙarfafa mahalarta su ba da gudummawa don wayar da kan jama'a game da kalubalen muhalli.
Misali
: Shirin Bambancin Harsuna
An ƙaddamar da shirin bambancin harsuna don inganta bayanan bayanai na hotunan abubuwan al'adu, al'adu، da wuraren tarihi. Masu tsarawa sun kafa kamfen da ke da niyya ga takamaiman al'ummomin harsuna don wadatar da bayanan da aka tsara da harsuna da yawa akan Wikimedia Commons. Mahalarta sun ba da gudummawa ta hanyar ƙara rubutun kalmomi da kwatance a cikin harsuna daban-daban, inganta wakilcin duniya na abubuwan al'adu.
Misali
: Haɗin gwiwar Cibiyoyin Ilimi
Cibiyar ilimi tana aiki tare da ISA don shigar da dalibai cikin kamfen ɗin inganta bayanai. Cibiyar ta kirkiro kamfen ɗin da aka mayar da hankali kan hotuna masu dacewa da tsarin karatun ta, Kamfen ɗin yana haɓaka haɗin gwiwa tsakanin ɗalibai da malamai, ƙirƙirar ƙwarewar ilimi mai mahimmanci yayin da yake ba da gudummawa ga Wikimedia Commons.
Misali
: Gasar daukar hoto ta yanayi
Ana amfani da ISA don gasar daukar hoto ta yanayi, inda mahalarta ke ba da gudummawa don inganta bayanan bayanai don hotunan da aka kama a lokacin takamaiman yanayi. Masu tsarawa suna shirya kamfen don yanayi daban-daban, suna ƙarfafa mahalarta su ƙara cikakkun kalmomi da nunawa. Gasar ta haifar da sha'awa tsakanin masu daukar hoto da masu sha'awar metadata, davhaifar da haɗin gwiwar al'umma.